14 Nuwamba 2020 - 11:11
​Za’a Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga Ta Goyon Bayan Trump A Washington

Kakakin fadar white House ta kasar Amurka ta bada sanarwan cewa a yau Asabar ce masu goyon bayan shugaban kasar Donal Trump zasu fito zanga-zanta ta miliyoyin mutane a birnin Washington don nuna goyon bayansu ga shugaban.

ABNA24 : Kayleigh McEnany ta bayyana haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa a yau asabar ce miliyoyin masu goyon bayan shugaban kasar mai ci Donal Trump zasu gudanar da zanga-zanga ta nuna goyon bayansu gareshi da kuma matsayin da ya dauka dangane da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba da muke ciki.

McEnany ta kara da cewa za’a fara zanga-zangar daga fadar white house har zuwa babban kotun kasar don tabbatar da bukatarsu ga babban kotun ta shiga tsakani don fayyace wanda ya lashe zaben shugana kasa na shekara ta 2020.

Kafafen yada labarai a duk fadin kasar sun ba da sanarwan cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrate Joe Biden ne ya lashe zaben na ranar Talata babba.

Shugaban Trump dai ya ki amincewa da sakamakon zaben. Sannan ya bukaci a sake irgen wasu kuri’an a wasu jihohin da aka ce Biden ya ci zaben. Sai dai hukumomin zabe a Jihar Pensulvenia sun ce ba za su sake irgen kuri’un da aka rika aka kirga a jihar ba.

342/